Babban magana: Lauyoyin Edo sun kauracewa kotu kan sace wata mai shari’a

Babban magana: Lauyoyin Edo sun kauracewa kotu kan sace wata mai shari’a

- Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Benin, sun fara yaji na kauracewa kotuna na tsawon kwanaki uku daga yau Laraba

- Hakan ya kasance zanga-zanga a kan garkuwa da Justis Chioma Iheme-Nwosu da aka yi

- Shugaban kungiyar lauyoyin reshen Benin, Collins Ogiebgean, ya ce za su cigaba da kauracewa kotuna har zuwa ranar Juma’a

Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Benin, a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba, sun fara yaji na kauracewa kotuna na tsawon kwanaki uku.

Kauracewa kotunan da lauyoyin ke yi ya kasance zanga-zanga a kan garkuwa da Justis Chioma Iheme-Nwosu da aka yi.

Channels Talevision ta ruwaito cewa a lokacin da wakilinta ya ziyarci harabar kotu a jihar, sai ya lura cewa dukkanin dakunan kotun a rufe suke da makulli. Hakazalika kotun Majistare na Evboriaria dake birnin jihar ma ya kasancebabu lauyoyi.

Shugaban kungiyar lauyoyin reshen Benin, Collins Ogiebgean, ya ce za su cigaba da kauracewa kotuna har zuwa ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa idan har zuwa lokacin ba a saki mai shari’an da aka sace ba, toh mambobin kungiyar ba su da zabin da ya wuce tsawaita wa’adin kauracewa kotunan.

“Idan har za a iya garkuwa da alkalai a rana tsaka, ina ga mu? Wannan ne dalilin da yasa muka yanke shawarar zanga-zanga ta hanyar kauracewa kotu,” inji Ogiebgean.

An yi garkuwa da Justis Nwosu-Ihme a makon da ya gabata a birnin Benin yayinda take a hanyar zuwa kotu. Mai shari’an ta kotun daukaka kara na Benin ta kasance mai shari’a mace ta farko a Najeriya da ta karanci fannin Shari’a har zuwa mataki na Ph.D.

KU KARANTA KUMA: Babu rashin jituwa tsakanin Buhari da Osinbajo – Fadar Shugaban kasa

Garkuwa da aka yi da ita na zuwa ne yan kwanai kadan bayan masu garkuwa da mutane sun saki Alkalin babbar kotun tarayya da ke Akure, jihar Ondo, Justis Abdul Dogo, wanda aka sace a iyakar dake tsakanin jihohin Edo da Ondo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel