El-Rufai ya kara nada sabbin hadimai guda 18 a fadar gwamnatin Kaduna

El-Rufai ya kara nada sabbin hadimai guda 18 a fadar gwamnatin Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi wasu sabbin nade naden hadimai masu muhimmanci a gwamnatinsa da zasu taya shi gudanar da ayyukansa da manufofinsa wajen cika ma jama’an jahar Kaduna alkawurran daya daukan musu.

Kaakakin gwamnan jahar Kaduna, Muyiwa Adekeye ne ya sanar da wadannan sabbin nade inda yace gwamnan Kaduna ya amince da nadin tsohon babban ma’aikacin jaridar Daily Trust, Malam Ibraheem Shehu a matsayin mataimaki na musamman a harkar kafafen watsa labaru da hulda da jama’a.

KU KARANTA: Manyan nasarori 7 da na samu a matsayin shugaban NNPC – Mele Kyari

Shi dai Malam Ibraheem Shehu ya kasance ya taba aiki a kwamitin karbar mulki ta jam’iyyar APC, haka zalika ya kasance guda daga cikin membobin kwamitin yakin neman zabe na jam’iyyar APC.

A hannu guda kuma, Gwamna El-Rufai ya amince da nadin karin hadimai da suka hada da:

1 Stella Amako – Mashawarciya ta musamman a kan hulda da al’ummai

2 Zainab Shehu - Mashawarciya ta musamman a kan cigaban al’umma

3 Aliyu Haruna – Babban mataimaki na musamman a kan matasa

4 Ibrahim Isma’il - Babban mataimaki na musamman a kan hulda da jama’a

5 Hafsat Aminu Ashiru - Babbar mataimakiya na musamman a kan harkar mulki a ofishin mataimakiyar gwamna

6 Nazir Sunusi - Mataimaki na musamman a kan kimiyya da fasaha

7 Mohammed Bello Shuaibu - Babban mataimaki na musamman a kan masu ruwa da tsaki

8 Yakubu Yatai - Mataimaki na musamman a kan hulda da al’umma

9 Ashiru Zuntu - Mataimaki na musamman a kan hulda da al’umma

10 Rabi Musa Manchi – Mataimakiya ta musamman a harkar sharia

11 Mahmud Mahmud Aminu - Mataimaki na musamman a harkar sharia

12 Aminu Lawal Na-Anty – Mataimaki na musamman a kan harkokin matasa

13 Sonia Bature – Mataimakiya ta musamman a kan harkokin muhalli

14 Kamal Aliagan – Mataimaki na musamman a kan wayar da kawunan jama’a

15 Sakinat Bello - Mataimakiya ta musamman a kan harkokin muhalli

17 Mohammed Jalal

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel