Babu rashin jituwa tsakanin Buhari da Osinbajo – Fadar Shugaban kasa

Babu rashin jituwa tsakanin Buhari da Osinbajo – Fadar Shugaban kasa

Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin cewa akwai wani rashin jituwa a tsakanin ofishin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Babban mai ba Shugaban kasa shawara na musamman akan harkokin majalisar dokokin tarayya, Sanata Babajide Omowurare ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai a majalisar dokokin tarayya.

Da yake martani ga masu sukar lamari wadanda suka dasa ayar tambaya akan hukuncin shugaba Buhari na sanya hannu a wata doka a Landan, Sanata Omowrare ya ce lallai kundin tsarin mulki ta ba Shugaban kasar damar aiki daga ko ina.

Ya yi bayanin cewa lamarin ya sha banban da na tsohon Shugaban kasa Umaru YarAdua da mataimakin Shugaban kasa Goodluckk Jonathan inda ta kai ;lokacin da tsohon Shugaban kasar baya iya aiwatar da ayyukansa saboda tsananin rashin lafiya.

Sai dai kuma ya yi gum da bakinsa kan dalilin da yasa Shugaban kasar bai aika wata wasika zuwa ga majalisar dokokin kasar ba, inda zai mika ragamar aiki zuwa ga mataimakin Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kwana daya bayan ya rattaba hannu a gyararren dokar harajin hakar danyen man fetur dake cikin rafi a Landan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sallamar akalla 35 cikin hadimai sama da 80 a ofishin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

An tattaro cewa hadiman da lamarin ya shafa, wadanda aka baiwa takardar kama aiki a watan Agusta, sun hada wasu manyan hadimai na mussaman, masu bayar da shawara na mussaman, da hadimai na fasaha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel