Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

An tattaro cewa an fara zaman ne da misalign karfe 11:00 na safe a zauren majalisar da ke fadar Shugaban kasar.

Zaman ya kasance na biyu da Osinbajo ke jagoranta tun bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar kasar a ranar 28 ga watan Oktoba.

Da fari dai Buhari ya halarci wani taro ne a kasar Saudiyya sannan a yanzu haka yana ziyarar sa-kai a birnin Landan.

Ana sanya ran dawowarsa gida Najeriya a ranar 17 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA KUMA: PDP ta sha kaye a karar da ta daukaka kan Sanata Gobir, da yan majalisar wakilai 3 na APC a Sokoto

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kwana daya bayan ya rattaba hannu a gyararren dokar harajin hakar danyen man fetur dake cikin rafi a Landan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sallamar akalla 35 cikin hadimai sama da 80 a ofishin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

An tattaro cewa hadiman da lamarin ya shafa, wadanda aka baiwa takardar kama aiki a watan Agusta, sun hada wasu manyan hadimai na mussaman, masu bayar da shawara na mussaman, da hadimai na fasaha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel