Yanzu-yanzu: Kotu ta fitittiki babban sanatan APC, ta baiwa PDP kujerar

Yanzu-yanzu: Kotu ta fitittiki babban sanatan APC, ta baiwa PDP kujerar

Kotun zaben majalisar dattawa a jihar Ekiti ta fitittiki kakakin majalisar kuma babban jigon jam'iyyar APC, Sanata Dayo Adeyeye, daga kujerarsa a hukuncin da ta yanke ranar Laraba, 6 ga Nuwamba, 2019.

Kotu ta umurci hukumar gudanar da zabe INEC ta baiwa Sanata Biodun Olujimi, ta jam'iyyar PDP saboda itace sahihiyar mai nasara a zaben.

Sanata Adeyeye yana wakilta mazabar Ekiti ta kudu.

Wannan shine babban rashi na hudu da jam'iyyar APC za ta samu cikin makon nan a majalisar dokokin tarayya.

DUBA WANNAN Ana ba Maina beli guduwa zai yi daga Najeriya - EFCC ta laburtawa kotu

Na farko shine kwace kujerar sanata mai wakilta mazabar Sokoto, Tambuwal, kuma ta baiwa dan jam'iyyar PDP.

A ranar Litinin, Kotun daukaka kara dake zaune a jihar Kaduna a ranar Litinin ta fitittiki dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltan mazabar Tudun Wada/Doguwa kuma shugaban masu rinjaye a majalisa, Alhassan Ado Doguwa.

Kotun ta yi watsi da zaben kananan hukumomi biyu da Ado Doguwa ke wakilta kan zargin magudin da aka tafka a zaben Febrairun 2019 kuma ta bada umurnin gudanar da saon zabe.

Hakazalika kotun zabe ta kori dan majalisa mai wakiltan Kiru/Bebeji, Abdul Mumuni Jibrin, daga kujerarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel