Daga Amalala: Yayarta tayi mata mugun dukan da yayi ajalinta

Daga Amalala: Yayarta tayi mata mugun dukan da yayi ajalinta

Wata yarinya mai shekaru 13 ta mutu har lahira bayan dukan da yayarta tayi mata sakamakon fitsarin kwance da ta tsula.

Precious Omenka, mai shekaru 13 a duniya ta kaiwa yayarta wacce suke uba daya mai suna Nneka ziyara kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Emeka Omenka, mahaifin yarinyar da ta rasu, yace ya haifi Nneka ne lokacin suna soyayya da mahaifiyarta Seki Eko. Daga baya ne ya auri matarsa Ifeoma wacce ta raini Nneka kamar 'yarta saboda rashin haihuwar da ta bata yi ba da wuri.

Emeka Omenka ya bayyana yadda Nneka ta takura har sai da ya bar Precious ta kai mata ziyara a Ikota, Lekki a ranar 12 ga watan Oktoba. Kwatsam ranar 16 ga watan Oktoba sai aka dawo mishi da Precious a wahalce kuma tana koken jikinta na ciwo. Ta sanar da iyayenta cewa, Nneka da mahaifiyarta Seki Eko sun zaneta saboda tayi fitsarin kwance.

Omenka yace, Precious tayi bayanin yadda suka haureta a ciki, kirji da sauran sassan jikinta. Ta kara da bayyanawa iyayen cewa sun zaneta da sanda da kuma wayar wuta.

An garzaya da Precious asibitin tarayya da ke Ebute Metta inda ta mutu a ranar 25 ga watan Oktoba bayan jinyar dukan da yayarta da mahaifiyarta suka mata.

DUBA WANNAN: Fallasa: An gano yadda Abba Kyari ya ingiza Buhari ya kwace aikin kaddamar da NLTP

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, shaidar mutuwar Precious daga asibitin sun nuna cewa, ciwon koda da zuciya ne suka yi ajalinta.

Yayin maida martani akan mutuwar yarsa, Omenka yace: "Ina cikin tsananin bakin ciki. Nneka 'yata ce da na haifa da Seki Edo amma ban aureta ba. Mahaifiyar Precious ta rike Nneka kamar 'yar cikinta amma a yau ta kashe mata 'yarta daya kwal a duniya."

"Lokacin da na auri Ifeoma, bata samu haihuwa da wuri ba a don haka ta rike Nneka kamar 'yarta. Ko lokacin da ta nemi in bar Precious ta kai mata ziyara, banda ta cewa. Saboda a tunanina duk daya suke. Mijinta na zama a Dubai, tayi alkawarin sanya Precious a makarantar kudi saboda nuna godiyarta ga mahaifiyarta."

Tuni dai mahaifin yaran ya mika kokensa ga hukumar 'yan sandan jihar Legas don bi masa hakkin mutuwar 'yarsa.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma yace tuni an cafke wacce ake zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel