Masu garkuwa da mutane sun kashe abokai biyu bayan karbar kudin fansa

Masu garkuwa da mutane sun kashe abokai biyu bayan karbar kudin fansa

Wasu masu garkuwa da mutane sun kashe abokai biyu a Kaduna bayan karbar kudin fansa har naira miliyan 2.1 daga danginsu.

An gano cewa, zukatan mazauna Hayin Banki a Kaduna sun shiga rudani a jiya bayan da suka gano an kashe Alhaji Abdullahi Kabiru da abokinsa, Alhaji Sanusi Dabai kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

An sacesu ne a yankin Kangimi dake Turunku, babban birnin karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna kusan kwanaki 12 da suka gabata.

Dan marigayi Alhaji Kabiru, Mohammed Dikko, ya sanar da wakilin Daily Trust da ya kai ziyara gidansu cewa, 'yan sintiri ne suka gano gawar mahaifinsa da ta abokinsa bayan kuma sun biya kudin fansa kwanaki kadan da suka gabata.

DUBA WANNAN: Ire-iren abinci 5 da ya kamata dan adam ya guda kafin kwanciya barci

"Koda wadanda suka yi garkuwa dasu suka kiramu, sun bukaci miliyan biyar ne amma sai muka Samar dasu bamu da wannan kudin. A haka muka daidaita akan naira miliyan biyu. Sun kuma bukaci dubu dari ta kudin kati wanda muka hada muka basu," in ji shi.

Dikko yace bayan sun bada kudin ne masu garkuwa da mutanen suka kirasu suka ce wannan kudin na ciyarwa ne don haka ba zasu saki iyayen nasu ba.

"Bayan kwanaki biyu ne muka bukaci taimakon 'yan sintiri duk da harda 'yan sanda suna kokarinsu. Kwatsam sai ga gawawwakinsu a daji," in ji Dikko.

Ya kara da cewa, 'yan sandan sun cafko masu garkuwa da mutane 12 a dajin yayin neman.

Wani daga iyalan Dabai, wanda bai bayyana sunansa ba, yace duk da tsananin rudani da suka shiga, sunyi imanin kowa ma zai koma ga Ubangijinsa.

Anyi kokarin ganawa da mai magana da yawun 'yan sandan jihar Kaduna, DSO Yakubu Sabo, amma hakan ya ci tura don baya daukar wayarsa har a lokacin da aka rubuta wannan rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel