Duk Mai Rigima Da Ganduje Ya Na Batawa Kan Sa Lokaci Ne Kawai - Ministan Tsaro, Magashi

Duk Mai Rigima Da Ganduje Ya Na Batawa Kan Sa Lokaci Ne Kawai - Ministan Tsaro, Magashi

Cikin wata annashuwa da tabbatar da abinda ya ke magana a kai, Ministan Tsaron kasar nan, Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya) ya jinjinawa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Magashi yace: "Yau dai a Kano duk wani wanda ya ce zai rigima da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje to kuwa ya na batawa kan sa lokaci ne kawai. Ba wata tantama a wannan maganar."

"Shugaba ne da ya san mutuncin mutane, ya iya mu'amala ta mutuntaka da mutane. Ba tare da yin la'akari da matsayin mutum ba."

Ya yi wannan furici ne a daren yau Asabar lokacin wata liyafar cin abincin dare da Gwamna Ganduje ya shiryawa duk wadanda a ka ba wa mukamai a cikin gwamnatin tarayya, a wannan karon mulkin na biyu na Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a dakin taro na "Africa House" a fadar gwamnatin jihar Kano.

DUBA WANNAN: Ba zai yiwu ba - Kamfanonin sadarwa sun mayarwa minista Pantami martani kan rage kudin Data

Janar Magashi ya ci gaba da cewa shi gwamnan na Kano, shugaba ne nagari wanda ya san yakamata, kuma ya san menene ya dace da jama'arsa na ci gaban al'ummarsa.

Cikin wani yanayi na gamsuwa da yadda gwamnan yake tafiyar da mulkin jihar kuma, Ministan Tsaron ya ce su duka wadanda gwamnatin tarayyar ta ba su mukamai, za su hada hannu waje daya domin ganin sun tallafawa harkar cigaban jihar gaba daya, ba tare da yin kasa a gwiwa ba kuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel