Wata sabuwa: Shugaba Buhari ya fatattaki hadimai 35 a ofishin Osinbajo

Wata sabuwa: Shugaba Buhari ya fatattaki hadimai 35 a ofishin Osinbajo

Kwana daya bayan ya rattaba hannu a gyararren dokar harajin hakar danyen man fetur dake cikin rafi a Landan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sallamar akalla 35 cikin hadimai sama da 80 a ofishin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

A yanzu haka shugaban kasar na a Landan, kasar Ingila inda ya kai ziyarar makonni biyu sannan ana sanya ran dawowarsa Abuja a ranar 17 ga watan Nuwamba.

An tattaro cewa hadiman da lamarin ya shafa, wadanda aka baiwa takardar kama aiki a watan Agusta, sun hada wasu manyan hadimai na mussaman, masu bayar da shawara na mussaman, da hadimai na fasaha.

Wasu majiyoyi abun dogaro wadanda suka nemi a sakaya sunayensu sun ce akwai yiwuwar ba hadiman wasikar sallamarsu a ranar Laraba.

A yayinda ake shirin sallamarsu, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an tura hadiman zuwa wasu ma’aikatu da suka yi daidai da fanninsu a watan da ya gabata. An yi zargin cewa yunkurin na da nasaba da kokarin hana su samun shiga fadar Villa da kuma rage karfin mataimakin Shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Fallasa: An gano yadda Abba Kyari ya ingiza Buhari ya kwace aikin kaddamar da NLTP

Sai dai kuma kakakin shugaban kasa, Garba Shehu da na mataimakin Shugaban kasar, Laolu Akande, sun ki amsa sakon waya da aka tura masu domin jin ta bakinsu kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel