Manyan nasarori 7 da na samu a matsayin shugaban NNPC – Mele Kyari

Manyan nasarori 7 da na samu a matsayin shugaban NNPC – Mele Kyari

Shugaban hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC, Malam Mele Kyari ya bayyana cewa hukumar NNPC ta kammala kashi na farko na aikin gyarar matatar man fetir dake garin Fatakwal, jahar Ribas.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Kyari ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin wani taron babban zaure a babban birnin tarayya Abuja inda yake zayyana irin nasarorin daya samu tun bayan hawansa mukamin shugabancin NNPC.

KU KARANTA: Dan Najeriya ya soka ma dan Najeriya wuka a kasar India a kan kwanon abinci

Kyari ya bayyana wasu daga cikin nasarorin daya samu sun hada da: kammala kashi na farko na gyarar matatar main a Fatakwal, tsimin kimanin dala biliyan 3 a sashin shari’a na hukumar, hako mai tafkin Kolmani a jahar Bauchi da kuma tara fiye da litan mai biliyan 2.

Sauran nasarorin da shugaban NNPC Mele Kyari ya bayyana a matsayin nasarorin daya samu sun hada da; Sake bude rijiyar man fetir ta Oil Mining Lease (OML 25) bayan kwashe shekaru 2 a garkame sakamakon rikici tsakanin jama’an yankin da kamfanonin main a Belema da Shell.

Bugu da kari wata babbar nasara da NNPC ta samu a karkashin jagorancin Kyari shi ne rattafa hannu kan sabuwar kwangila tsakanin kamfanin Agip da hukumar cigaban albarkatun man fetir na Najeriya, NPDC inda Agip ta mika ma NPDC rijiyoyin mai 3.

Haka zalika Kyari yace sun samu nasarar samun zuba jarin dala biliyan 3.15 a rijiyar mai ta OML 13 da kuma dala miliyan 876 a rijiyar mai OML 65.

A yayin ganawar, Kyari ya bayyana wani sabon tsarin ciyar da hukumar gaba ga ma’aikatan NNPC, watau tsarin TAPE-Transparency, Accountability and Performance Excellence.

Daga karshe Kyari ya yi kira ga ma’aikatan hukumar NNPC su ninka kokarin da suke yi domin ganin Najeriya ta ci ribar arzikin albarkatun man fetir da Allah Ya yi mata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel