Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya fi mataimakin shugaban kasa karfin iko - Akin Alabi

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya fi mataimakin shugaban kasa karfin iko - Akin Alabi

- Honarabul Akin Alabi ya ce ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ta fi ofishin mataimakin shugaban kasa karfi da iko a tsarin mulki irin ta Najeriya

- Dan majalisar tarayyar ya yi wannan furucin ne kan cece-kuce da ake yi kan saka hannu kan doka da Shugaba Buhari ya yi a Landan duk da cewa mataimakinsa na Najeriya

- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya garzaya har zuwa birnin Landan don mika takardu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari don yasa hannu

Wani dan majalisar wakilai, Akin Alabi, ya ce ofishin Abba Kyari ya fi karfi da kafuwa fiye da na mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Alabi, dan jam'iyyar APC, ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba a shafinsa na Tuwita.

DUBA WANNAN: Okorocha ya bayyana abinda zai faru da APC bayan 2023

Dan majalisar mai wakiltar Egbeda da Ona Ara a jihar Oyo ya mayar da martani ne ga 'yan Najeriya da ke kalubalantar Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan saka hannu da yayi a dokar bayan baya Najeriya kuma mataimakinsa na kasar.

A wannan tafiyar da shugaban kasar yayi, yaki mika karagar mulkin kasar ga mataimakinsa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Alabi, wanda dan kasuwa ne kuma dan siyasa ne, ya ce shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasan a halin yanzu shine mataimakin shugaban kasan.

Ya wallafa a shafinsa cewa, "Shugaban kasa na kokari wajen aiwatar da aiyukansa da kuma wadanda aka sa shi."

Wannan kuwa ya jawo maganganu daga 'yan Najeriya ma'abota amfani da kafar sada zumuntar ta tuwita.

Wasu sun goyi bayanshi inda wasu suka kalubalanceshi.

Amma kuma shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya maida martani akan hakan inda yake cewa, shugaban kasa Buhari zai iya jagorantar duk lamurran kasar nan ko ina kuwa yake a fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel