Kun san inda yan Boko Haram suke – Gwamna Borno ga jami’an tsaron Najeriya

Kun san inda yan Boko Haram suke – Gwamna Borno ga jami’an tsaron Najeriya

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa kowa ya san inda mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suke zama, don haka abin da kawai ya rage shi ne a far musu.

Jaridar This Day ta ruwaito Zulum ya bayyana haka ne a ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba a yayin wani babban taron tsaro da babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Adamu ta shirya a jahar Borno.

KU KARANTA: Dan Najeriya ya soka ma dan Najeriya wuka a kasar India a kan kwanon abinci

“Duk mun san wadannan miyagun mutanen, Sojoji, hukumomin tsaro, masu rike da sarautun gargajiya, kai hatta jama’an gama gari sun inda yan ta’addan suke, don haka abinda ya kamata mu kai musu farmaki a gidajensu.

“Abinda ya kamata mu sani shi ne rashin zaman mutane a wasu garuruwan shi yasa ake cigaba da fuskantar matsalar tsaron, don haka bai kamata wani gwamna a yankin Arewa maso gabas ya bari yan Boko Haram su sake fatattakar jama’a daga garuruwansu ba.” Inji shi.

Haka zalika gwamnan ya jaddada manufarsa na taimaka ma hukumomin tsaro da Sojojin Najeriya don ganin sun karya yan ta’addan gaba daya.

Shi ma gwamnan jahar Yobe, Mai Mala-Buni ya yi kira ga hukumomin tsaro dasu samar da wani sabon salon yaki da ta’addanci ta hanyar amfani da sulhu, tunda dai matakin Soji bai haifar da Da mai ido ba.

Bugu da kari, wakilin shugaban kasa majalisar dattawa a wannan taro, kuma shugaban kwamitin majalisar dattawan Najeriya a mai sanya idanu a kan rundunar Sojan kasa, Sanata Ali Ndume ya koka kan karancin kudaden aiki da Sojoji suke samu da kuma karancin adadin Sojojin Najeriyan kansu.

A cewar Sanatan, rundunar Sojan kasa na da hafsoshin Soja 6,000 da kuma kuratan Sojoji 154,000, a maimakon Sojoji 400,000 daya kamata a ce akwai a kasa kamar Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel