Shan abarba na rage yiwuwar kamuwa da sutar 'kansa' - NIHORT

Shan abarba na rage yiwuwar kamuwa da sutar 'kansa' - NIHORT

Cibiyar bincike kan ilimin shuke-shuke wato National Horticultural Research Institute (NIHORT) ta ce yawan shan Abarba na rage yiwuwar kamuwa da cutar daji kuma yana sa saurin warkewa daga jinyar tiyata.

Shugaban NIHORT, Dr Abayomi Olaniyan, ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da cibiyar raya Abarba a Owo, karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Diraktan, wanda ya smau wakilcin Dr Olutola Oyedele, diraktan binciken NIHORT, ya ce Abarba babbar kayan itace ce mai muhimmanci ga lafiyar jiki da kuma tattalin arzikin kasa.

Yace: "Abarba na kunshe da sinadarai da dama na inganta garkuwa jiki. Yawan shan Abarba na sa saurin warkewa daga jinyar tiyata kuma yana taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da cutar kansa."

A wani binciken daban, Wani sabon bincike na kwararrun kiwon lafiya da aka fitar ya bayyana cewa, kamar yadda barasa ke illata hantar dan Adam, hakazalika yawaita ta'ammali da sukari na tsawon lokaci ya kan kawo lahani na ban mamaki ga hantar ta dan Adam.

Duk da cewar kayan abinci da na sha masu zaki na da matukar dandano mai bankaye akan harshe, tare da nishadantar da mai ta'ammali da su, su kan lalata hakori; tare da haddasa cututtukan da suke hadar da; ciwon zuciya, mutuwar barin jiki, kansa wato cutar daji da kuma lahani ga hanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel