Ki mayar masa da kudaden da kika karba hannunsa - Alkali ya umurci budurwar da ta jizga saurayi bayan an sa rana

Ki mayar masa da kudaden da kika karba hannunsa - Alkali ya umurci budurwar da ta jizga saurayi bayan an sa rana

Kotu dake zaune a unguwar Gudu a birnin Abuja ta umurci wata budurwa yar shekara 22, Aisha Shettima, ta nemi saurayinta da ta yaudara domin su tattauna kan yawan kudinsa da zata mayar masa dashi tun da ta fasa aurenshi.

Alhaji Shehu Marafa, ya shigar da Aisha Shettima kara kotu inda ya bukaci kotun ta umurceta ta dawo masa da N500,000 da ta karba hannunsa domin shirye-shiryen aure.

Alkalin kotun Ado Mukhtar ya umurci Aisha ta biya Marafa kudinsa da ta karba tun da ta fasa aurensa.

Alkalin ya bada umurnin ne bayan Alhaji Marafa ya ki karban kayayyakin da Aisha Shettima tayi ikirarin cewa ta saya da kudin.

Yace: "Tunda ya ki karban kayayyakin, ki biyashi kudinsa,"

Alkalin ya dage karan zuwa ranar 18 a Nuwamba.

Alhaji Marafa yace: "Na bata N200,000 na kudin kayayyakin da zata siya, sannan na tura N300 asusun bankinta."

"A watan Febrairu na tafi jihar Bauchi gaishe da iyayenta kuma na biya N50,000 kudin sadaki kuma na baiwa iyayen N20,000 da kwandon goro da alewa matsayin baiko."

"Bayan baiko, an sa rana 27 ga Afrilu, daurin aure. Sai ta kira ni makonni biyu bayan haka cewa ta fasa saboda ba ta sona."

"Mahaifinta ya dawo da N70,000 na sadaki da kyautan da nayi musu lokacin gaisuwan amma Aisha ta ki dawo da N500,000 da na bata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel