Fallasa: An gano yadda Abba Kyari ya ingiza Buhari ya kwace aikin kaddamar da NLTP

Fallasa: An gano yadda Abba Kyari ya ingiza Buhari ya kwace aikin kaddamar da NLTP

- An dade ana yada jita-jitar cewa wasu manyan hadiman shugaban kasa, Muhammadu Buhari, suna cin fuskar Osinbajo

- Jaridar Premium Times ta wallafa wani rahoto a kan yadda shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya wofantar da wata wasikar Osinbajo da ya aika wa Buhari

- Rahoton jaridar ya bayyana cewa Abba Kyari ya zuga Buhari ya cire Osinbajo daga shugabancin wani kwamiti da aka kafa domin warware rigimar makiyaya da manoma

A lokacin da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya rubuta wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wasikar neman izinin ya bar shi ya cigaba da jagorantar warware rikicin makiyaya da manoma a farkon shekarar 2019, bai yi tunanin cewa akwai wani mutum da zai datse wasikar ba har ma ya hana bukatarsa ganin hasken rana ba.

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya zama sanadin hana bukatar Osibajo shiga a wurin shugaba Buhari.

A cewar jaridar, ta gana da mutane tare da tattauna wa da wasu da ke da masaniya a kan siyasar cikin Villa, wadanda suka tabbatar mata da cewa bayan Abba Kyari ya wofantar da wasikar Osinabjo, bai tsaya iya nan ba, sai da ya ingiza Buhari ya cire Osinbajo daga shugabancin kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin sulhunta rikicin makiyaya da manoma.

DUBAWANNAN: Isa Zarewa: Tsohon sanata daga jihar Kano ya mutu a Abuja

Premium Times ta ce tana da wasu shaidu a hannunta da suke nuna irin cin fuskar da Osinbajo ke fuskanta a hannun wasu manyan hadiman shugaba Buhari, kamar yadda jita-jita ta dade da yadu wa a fadin kasa.

Jaridar ta kara da cewa takardun da ke hannunta sun nuna cewa shugaba Buhari ne ya dorawa Osinbajo daukan nauyin jagorantar shirin kafa wani tsarin kiwon dabbobi domin makiyaya (NLTP).

Gwamnatin tarayya ta bullo da tsarin NLTP ne bayan an sako shugaba Buhari a gaba a kan ya kawo karshen yawaitar rigingimun da ke faru wa tsakanin makiyaya da manoma, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 4,000 a shekarar 2016 da 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel