Me yayi zafi? Anyi musayar yawu tsakanin shugaban majalisar dattawa da magatakardan majalisa

Me yayi zafi? Anyi musayar yawu tsakanin shugaban majalisar dattawa da magatakardan majalisa

An ruwaito cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya fuskanci magatakardan majalisar dattawan, Mohammed Sani-Omolori akan zargin daukar aiki a majalisar ta bayan fage a taron da akayi na majalisar a ranar Litinin.

Wata majiya wacce ta sanar da wakilin jaridar The Punch, tace sunyi sabanin ne saboda rashin biyan alawus din tsoffin hadiman 'yan majalisar.

Majiyar tace, "Taron anyi shi ne a majalisar amma ya tashi babu dadi. Hatsaniyar ta fara ne lokacin da Lawan ya gayyaci magatakardan da yayi takaitaccen bayani akan dalilin da yasa ofishinsa ya gudanar da daukar aikin ta bayan fage ba tare da sanin hukumar majalisar ba."

Kamar yadda majiyar tace, Lawan yace ba a sanar da hukumar majalisar ba kafin fara diban ma'aikatan.

Majiyar ta kara da cewa, dattawan sun tada jijiyoyin wuya a taron har zuwa lokacin da suka gama musayar yawun.

DUBA WANNAN: Isa Zarewa: Tsohon sanata daga jihar Kano ya mutu a Abuja

An gano cewa, tsohon shugaban hukumar majalisar dattawan, Adamu Fika ya barranta kanshi daga daukar aikin. Yace, anyi lamarin ne ba tare da saninsa ba.

Hakazalika, daraktan yada labarai na majalisar dattawan, Rawlings Agada, ya musanta aukuwar hatsaniyar tsakanin Lawan da Sani-Omolori a taron.

Agada yace, "Nayi wa magatakardan magana akan al'amarin. Abinda zan iya cewa ya faru a taron shine, an tattauna akan maganar alawus din tsoffin hadiman ma'aikatan majalisar. Bansan wata matsala kuma da aka tattauna a majalisar ba."

"A yau Litinin, magatakardan da ministan kudi, kasafi da tsari, suka tattauna akan zancen alawus din tsoffin hadiman 'yan majalisar kuma sun shawo kan matsalar. Abinda na sani kenan." in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel