Wasu ‘Yan takarar Sanata sun janyewa Smart Adeyemi a Kogi

Wasu ‘Yan takarar Sanata sun janyewa Smart Adeyemi a Kogi

Gungun ‘yan takarar Sanata na yankin Kogi ta Yamma sun janye takararsu inda su ka marawa gwamna Alhaji Yahaya Bello da Abokin takararsa, Cif Edward David Onoja a zaben da za a yi.

Haka zalika ‘yan siyasan sun bayyana mubaya’arsu ga Sanata Smart Adeyemi wanda zai tsaya takarar kujerar majalisar dattawa. Za a yi zaben ne a Ranar 16 ga Watan Numwaban nan mai-ci.

‘Yan takarar sun tabbatar da mubaya’arsu ne a fili a lokacin da su ka yi wata zantawa ta musamman da 'Yan jarida a Garin Lokoja. An yi wannan hira ne a yau Talata, 5 ga Nuwamba.

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga Daily Trust, ‘yan takarar sun yi wannan jawabi ne tare da Jagororin yakin neman zaben su na duka kananan hukumomin jihar Kogi a zaben mai-zuwa.

KU KARANTA: Tsohon Sanatan Jam'iyyar PDP ya rasu a gidansa a Abuja

Wadanda su ka halarci zaman mubaya’ar sun hada da Olabode Adeyemi na jam’iyyar ADC, Princess Roseline Ibitoye na jam’iyyar Accord, da kuma Cif Samuel Atteh na jam’iyyar PPA.

Olasunkanmi Olayinka da Noah John Abiodun duk na jam’iyyun adawa su na cikin wadanda su ka yi alkawarin taimakawa jam’iyyar APC wajen lashe zaben gwamna da Sanatan da za ayi.

Adeyemi Olabode shi ne ya yi jawabi a madadin Takwarorinsa inda ya ce sun dauki wannan mataki ne domin cigaban jihar . ‘Yan takarar sun ce sun hakura da takararsu zuwa wani lokaci.

“A kan wannan mataki, mun umarci wakilanmu a duk rumfunan zabe da jagororin yakinmu su yi wa jam’iyyar APC mai mulki kamfe kuma su zabi duka ‘yan takarar ta a zaben 16 ga Wata.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel