Tambuwal: A dalilin siyasa na ajiye karatun Digirgir a UNIABUJA

Tambuwal: A dalilin siyasa na ajiye karatun Digirgir a UNIABUJA

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bada labarin yadda siyasa ta sa ya yi watsi da karatun Boko. Gwamnan ya ce saboda siyasa ya daina karatu a jami’ar tarayya da ke Abuja.

Mai girma Aminu Tambuwal ya ke cewa ya soma Digirgir watau 'Masters' a sha’anin shari’a a zangon 2002/2003, amma dole ya hakura da makarantar domin siyasa ya dauke masa hankali.

Gwamnan da ya zarce a kan mulki a jam’iyyar PDP bayan sauya-sheka daga APC, ya fadawa kungiyar Magatakardun jami’o’in da ke Najeriya bai yi da-na-sanin shiga siyasa a Duniya ba.

Rt. Hon. Aminu Tambuwal ya yi Digirinsa na farko ne a Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto inda ya karanta ilmin shari’a. A 1991, Tambuwal ya kammala jami’ar ya tafi aikin bautan kasa.

KU KARANTA: Buhari ya nada Mai bada shawara a kan harkar tattalin arziki

Bayan gwamnan na Sokoto ya tafi makarantar Lauyoyi, sai ya yi rajista domin fara Digirgir a Jami’ar UNIABUJA, amma ya gaza maida hankali a makarantar. Wannan ya faru ne a 2002.

“Lokacin da na fahimci cewa lallai ban iya cigaba da karatun ba, sai aka ba ni shawarar in nemi wani sojan gona ya rubuta mani jarrabawa, sannan kuma su yi mani aikin kundin bincike na.”

“Sai na ce ya fi yi mani alheri in hakura da karatun da girma da arziki, a kan in samu takardar shaidar Digiri na zir. A haka na bar jami’ar da mutunci na da daraja.” Inji Aminu Tambuwal.

Bayan tsohon shugaban majalisar wakilan ya bayyana cewa bai yi da-na-sanin matakin da ya dauka ba. Ya ce: “Watakila idan jami’ar jihar Sokoto ta fara Digirgir a shari’a in kara karatu.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel