Gwamnatin Buhari ta umarci kamfanonin sadarwa su rage farashin sayen Data

Gwamnatin Buhari ta umarci kamfanonin sadarwa su rage farashin sayen Data

Gwamnatin Najeriya ta umarci hukumar sadarwa ta Najeriya, NCC, ta tilasta ma kamfanonin sadarwar tare da samar da wani tsari da zai tabbatar da rage farashin sayen ‘Data’ da yan Najeriya suke yi, domin kuwa yan Najeriya na kokawa a kan tsadarsa.

Jaridar The Nation ta ruwaito ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami ne ya bayyana haka yayin da ya karbi bakuncin shuwagabannin gudanarwar hukumar NCC a karkashin jagorancin Sanata Olabiyi Durojaiye.

KU KARANTA: Dansanda ya harbi wani mutumi saboda ya auri budurwar da abokinsa yake so

Pantami ya bayyana ma bakin nasa cewa yan Najeriya da dama suna kai masa korafe korafe game da tsadar farashin sayen Data idan aka kwatanta da suaran kasashen nahiyar Afirka.

“Ina kira ga shugabancin NCC dasu tabbata su rage farashin sayen Data a Najeriya saboda yan Najeriya da dama suna kokawa game da tsadar Data, idan kuka je wasu kasashen, hatta kasashen da basu kai Najeriya yawan jama’a ba ma za ka ga cewa farashin Data bai kai namu ba.

“Ni kaina wannan matsalar ta shafeni, sai ka ga mutum yasa loda kati ya sayi Data, tun ma kafin ka yi amfani da kashi 20 na Datan kwatsam sai ga komai ya tafi.” Inji shi.

A wani labari kuma, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta kwace kimanin kudi naira biliyan 2.3 daga hannun tsohon shugaban hukumar kula da sayar da albarkatun man fetir ta Najeriya, PPMC, Haruna Momoh, ta mika ma gwamnatin tarayya.

Hukumar yaki da rashawa da makamantan laifuka, ICPC ce ta sanar da haka ta bakin kaakakinta, Rasheedat Okoduwa inda tace baya ga madaran kudin da kotu ta kwace, kotun ta kwace wasu kadarorinsa, inda ta mikasu dika ga gwamnatin tarayya a matakin wucin gadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel