Adalci: Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

Adalci: Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

- Wata kotu a jihar Kano ta yanke wa wani matashi, Abba Mustapha, mai shekaru 33 hukuncin kisa

- An gurfanar da matashin ne bisa zarginsa da kisan wani mutum ta hanyar bugunsa da fartanya

- Alkalin kotun, Jastis A. T Badamasi, ya ce ya yanke wa matashin hukuncin kisa saboda gamsuwa da hujjojin da lauyan gwamnati ya gabatar a kansa

Wata babbar kotu mai lamba ta 3 da ke zamanta a jihar Kano ta zartar hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi, Abba Mustapha, mai shekaru 33.

Ana zargin matashin ne da laifin kashe wani mutum mai suna Buhari Abubakar ta hanyar buga masa fartanya har ta kai ga hakan yayi sanadiyar mutuwarsa.

Matashin ya kashe Buhari ne sakamakon wani sabani da ya shiga tsakaninsu, shi kuma ya harzuka ya hau bugunsa da fartanya.

DUBA WANNAN: Zanga-zanga: Kungiyoyi 20 na Mata zalla sun mamaye majalisar dokokin jihar Kano

Yayin zaman kotun na ranar Litinin, alkalin kotun, Jastis A. T Badamasi, ya ce aifin da matashin ya aikata ya saba wa sashi na 221, a saboda haka ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Jastis Badamasi ya kara da cewa lauyan gwamnati, Zakariyya Muhammad, ya gabatar da hujjoji kwarara, masu karfi, a kan mai laifin da ake tuhuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel