Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da nade-naden Buhari na Justis Tsoho da Kanyip

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da nade-naden Buhari na Justis Tsoho da Kanyip

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da tabbatar da Justis Benedict Bakwaph Kanyip a matsayin shugaban kotun kasuwanci na Najeriya.

Legit.ng ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, wanda ya tabbatar da hakan a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, ya yiwa Justis Benedict fatan alkhairi a lokacin da zai kwashe yana shugabanci a kotun kasuwancin.

Haka zalika majalisar ta tabbatar da nadin Justis John Tsoho a matsayin babban alkalin babbar kotun tarayya.

An tabbatar da Tsoho ne biyo bayan wani rahoto da kwamitin majalisar dattawa kan shari'a karkashin jagorancin Sanata Michael Bamidele ya gabatar, inda ya bayar da shawarar tabbatar da nadin nasa.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da nade-nade 15 a hukumar NDDC

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr (Misis) Sarah Omotunde Alade, a matsayin mai ba Shugaban kasa shawara na musamman a kan harkokin kudi da tattalin arziki, inda za ta kasance a ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa.

Dr. Alade ta yi ritaya ne daga babban bankin Najeriya (CBN) a matsayin mataimakiyar gwamnan bankin a 2017. Ta kuma kwashe tsawon shekaru 23 tana aiki a babban bankin kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel