Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Sarah Alade a matsayin mai bashi shawara kan harkokin kudi da tattalin arziki

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Sarah Alade a matsayin mai bashi shawara kan harkokin kudi da tattalin arziki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr (Misis) Sarah Omotunde Alade, a matsayin mai ba Shugaban kasa shawara na musamman a kan harkokin kudi da tattalin arziki, inda za ta kasance a ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa.

Dr. Alade ta yi ritaya ne daga babban bankin Najeriya (CBN) a matsayin mataimakiyar gwamnan bankin a 2017.

Sabuwar hadimar shugaban kasar ta kwashe tsawon shekaru 23 tana aiki a babban bankin kasar.

Haka zalika Alade ta yi aiki a matsayin gwamnan CBN a 2014 na dan takaitaccen lokaci.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa shugaba Muhammadu Buhari ya nada Kyaftin Musa Nuhu a matsayin sabon Direkta-Janar na Hukumar Kula da Zirga-Zirgan jiragen Sama ta Kasa, NCAA.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da nade-nade 15 a hukumar NDDC

Mista Nuhu zai maye gurbin Kyafyin Mukhtar Usman a matsayin shugaban hukumar kamar yadda sanarwar da Jami'in Hulda da Al'umma na hukumar, James Odaudu ya fitar a Abuja a ranar Laraba.

Sabon shugaban na NCAA yana da digiri ta biyu (MSc) a fanin kasuwancin sufurin jiragen sama kuma yana daya daga cikin matukan jirage a tawagar shugaban kasa a matsayin Kyaftin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel