Daga zuwa kurkuku, Maina ya kamu da rashin lafiya, kotu ta daga zama

Daga zuwa kurkuku, Maina ya kamu da rashin lafiya, kotu ta daga zama

An samu cikas wajen gurfanar tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, AbdulRashid Maina, gaban alkalin babban kotun tarayya dake Abuja, Alkali Okon Abang, a yau Talata sakamakon rashin lafiya.

Hukumar EFCC ta kai karar Maina kotun ne kan zargin almundahana, babakere da yaudara na kudin fanshon jama'a kimanin Bilyan dari.

Yayinda kotu ta dawo zama yau Talata, jami'an hukumar gidajen yarin da sauya hali sun gabatarwa Alkalin kotun da wani takardar likitan gidan yarin mai suna, Idowu Ajayi, cewa Maina ya kamu da rashin lafiya.

Bayan karanta wasikar, Alkali Okon Abang, ya tambaye lauyoyin EFCC da na Maina ko sun san da rashin lafiyarsa, dukkansu sun ce basu da labari.

Bayan haka sai lauyan Maina ya bukaci kotun ta dakatad da zaman da mako daya domin ya samu lafiya.

Amma lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, ya bukaci kotun ta umurci mataimakin kwantrolan hukumar gidan yarin ya je ya duba Maina domin tabbatar da gaskiyan lafiyarsa.

Alkalin ya yanke cewa takardar Likita ba zai hana cigaba da gurfanar da shi ba saboda Likitan bai sa lokacin da ake kyautata zaton zai samu lafiya ba.

An dakatad da zaman zuwa ranar 7 ga Nuwamba, 2019.

A ranar 25 ga Oktoba, babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi umurnin tsare tsohon Shugaban hukumar fansho dake fuskantar shari’a, Abdulrasheed Maina, a gidan kurkuku.

Justis Okon Abang ya bayar da umurnin tsare shi biyo bayan wata bukata da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta nema bayan ya ki amsa tuhume-tuhume 12 ake yi masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel