Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da nade-nade 15 a hukumar NDDC

Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da nade-nade 15 a hukumar NDDC

Majalisar dattawa ta tabbatar da tsohon mataimakin gwamnan Edo, Dr. Pius Odubu da Bernard kumagba a matsayin Shugaba da manajan darakta na hukumar cigaban Niger Delta (NDDC).

Hakan ya biyo bayan rahoton kwamitin majalisar dattawa kan harkokin Niger Delta wanda Sanata Peter Nwoboshi ya jagoranta, wadanda sune suka tantance zababbun shugabannin.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bukaci zababbun shugabannin da su kare yardar da aka basu ta hanyar nada su sannan su yi aiki domin tabbatar da ganin mutanen Niger Delta sun daraja kudi.

Ya ce abun bakin ciki ne ganin hukumar NDDC ta shafawa kanta bankin fenti, wanda hakan ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari bayar da umurnin binciken hukumar da kyau.

Ya bukaci kwamitin majalisa dattawa kan harkokin Niger Delta da ta sanya idanu sosai sannan ta tabbatar da cewar ta lura da duk wani lamari na hukumar domin hana sake faruwar badakalar da aka yi a baya ta fannin gudanar da hukumar.

Sauran mutanen da majalisar ta tabbatar sun hada da matsayin babban daraktan ayyuka, Injiniya Otobong Ndem (Akwa Ibom) da babban daraktan kudi, Maxwell Okoh daga jihar Bayelsa.

Sauran sune wakilin jihar Delta, Prophet Jones Erue; Cif Victor Ekhator (Edo) da Nwogu Nwogu (Abia), Theodore Allison, mai wakiltan jihar Bayelsa, Victor Antai (Akwa Ibom); Maurice Effiwatt (Cross River); Olugbenga Elema (Ondo) da Hon. Uchegbu Chidiebere Kyrian (Imo).

KU KARANTA KUMA: Mun shiga fargaba don tsoron rushewar Kannywood - Falalu Dorayi

Hakazalika an tabbatar da wakilin arewa maso gabas, Ardo Zubairu daga jihar Adamawa, Ambassador Abdullahi Bage daga jihar Nasarawa domin ya wakilci arewa ta tsakiya, da kuma Aisha Murtala Muhammed, daga jihar Kano domin ta wakilci yankin arewa maso yamma.

Sai dai kuma, majalisar bata tabbatar da wakiliyar jihar Rivers, Dr. Joy Yimebe Nunieh ba, biyo bayan bayanin shugaban kwamitin na cewa bata gurfana domin tantance ta ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel