Rufe iyakokin Najeriya: Manoman shinkafa na darawa yayinda asusun su ke kara cika yana tumbatsa da kudade - Minista

Rufe iyakokin Najeriya: Manoman shinkafa na darawa yayinda asusun su ke kara cika yana tumbatsa da kudade - Minista

Rufe iyakokin Najeriya ya zaburar da hazikan manoman shinkafa a kasar wadanda a yanzu suke kan darawa sakamakon yawan kudaden da ke shiga asusun ajiyarsu na banki, karamin ministan noma da cigaban karkara, Mustapha Shehuri ya bayyana hakan.

A cewar wata sanarwa da aka tura wa manema labarai ministan ya yi bayanin ne a wani gidan kiwon dabbobi mallakar ma’aikatar gona ta tarayya da ke a Mando, Jihar Kaduna, a ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce: “Kudade sai shigo musu suke yi, su na ta garzayawa bankuna su na ajiya, saboda ana ci gaba da samun cinikin shinkafar mu da ake nomawa cikin gida Najeriya. Hakan kuwa zai kara samar da ayyukan yi ga matasa da kuma karfafa harkokin noma da kiwo da sauran harkokin masarufi daban-daban.”

Baya ga rufe kan iyakokin da ministan ya ce ya taimaka an karkato wajen cinikayyar shinkafar da ake nomawa a nan cikin Najeriya, ya kara da cewa tsare-tsaren bayar da tallafi da gwamnatin tarayya ke bai wa manoma ya kara inganta da karfafa noman shinkafa da sauran nau’o’in kayan abinci a cikin kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: CBN na yunkurin dawo da bashin N36bn daga manoma a arewa maso gabas

Ministan ya kuma jaddada cewa gwamnatin tarayya za ta raba wa kananan manoma kayan aikin gona yadda za a kara karfafa musu guiwa sosai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel