Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: hadarin kwale kwale ya halaka mutum 7 a Lafia

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: hadarin kwale kwale ya halaka mutum 7 a Lafia

Tabbas hadari ba sai a mota ba, wasu mutane 7 sun rigamu gidan gaskiya a dalilin kifawar wani kwale kwale a tafkin Gwayaka dake yankin gabashin garin Lafiya na jahar Nassarawa, inji rahoton Daily Trust.

Majiyarmu ta ruwaito wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yawancin wadanda hatsarin ya rutsa dasu manoman tumatir ne yan asalin jahar Kano da suka shiga gonakansu, suna hanyar komawa cikin gari da yammcin Juma’a a lokacin da lamarin ya auku.

KU KARANTA: Yansandan SARS sun kama wani mutumi saboda ya ajiye gemu, beli N50,000

Sai dai shaidan yace mutanen sun yi ma kwale kwalen yawa, sakamakon sun kai mutum 20, duk da matukin kwale kwalen, mutane 21, kuma sai da matukin ya nemi su bari ya fara daukan mutane 10, idan ya dawo ya dauki sauran, amma suka ki ya.

“Cikin fushi sai matukin jirgin yace ba zai tuka kwale kwalen ba, sai ya sauka daga kwale kwalen, nan take guda daga cikin fasinjojin ya yi dare dare a kan kwale kwalen ya fara tukasu, sai da suka raba tsakiyan tekun sai kwale kwalen ta kifa, 7 sun bace, da kyar sauran suka fito.” Inji shi.

Shaidan yace zuwa ranar Litinin sun samu gano gawarwakin mutane 3, amma har yanzu basu ga sauran gawarwakin ba.

Jami’in dake lura da yankin gabashin garin Lafiya, Shuaibu Dahiru Zanwa ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace suna ta kokarin ganin sun gano sauran gawarwakin guda 4, haka nan zasu tattauna da garuruwan dake gabar tekun domin magance sake aukuwar lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel