Kotu ta mika ma gwamnati naira biliyan 2.3 da tsohon shugaban PPMC ya sata

Kotu ta mika ma gwamnati naira biliyan 2.3 da tsohon shugaban PPMC ya sata

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta kwace kimanin kudi naira biliyan 2.3 daga hannun tsohon shugaban hukumar kula da sayar da albarkatun man fetir ta Najeriya, PPMC, Haruna Momoh, ta mika ma gwamnatin tarayya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito hukumar yaki da rashawa da makamantan laifuka, ICPC ce ta sanar da haka ta bakin kaakakinta, Rasheedat Okoduwa inda tace baya ga madaran kudin da kotu ta kwace, kotun ta kwace wasu kadarorinsa, inda ta mikasu dika ga gwamnatin tarayya a matakin wucin gadi.

KU KARANTA: Matashi ya tubure a kan N99,000 da aka aika masa bisa kuskure ta asusun bankinsa

ICPC ta zargi Momoh da tara dukiyar ne ta haramtacciyar hanya, inda tace kadarorin da kotun ta kwace sun hada da Plot 199, Ebitu Ukiwe Street, Utako, Nos. 21, 22, 23 and 26 Olympia Estate, Kaura District, Plot 1824, Cadastral Zone, BO7, Katampe, plot 1827, Cadastral Zone, BO7, Katampe da No. 6 Casamance street, Wuse Zone 3 dukansu a Abuja.

Haka zalika hukumar ta zargi Momoh da keta alfarmar kujerarsa, inda ya yi amfani da abokansa da kamfanonin Shell wajen karkatar da kudaden gwamnati domin amfanin kansa, musamman wajen neman kwangila daga NNPC, ba tare da ya gudanar da kwangilar da aka bashi ba kuma.

Bugu da kari hukumar ICPC ta binciko wasu asusun banki guda 4 a bankin UBA, mallakin uwargidar Haruna Momoh dauke da makudan kudade da suka kai naira miliyan 496.2 a naira da kudaden kasashen waje, haka zalika sun gano wani asusun bankin Union dake da dala miliyan 1.7 da N496.2m

”ICPC ta sake bankado wasu Euro 173, 601.55, $5, 563.21 da N876, 209, 744 a asusun banki guda uku na bankin Stanbic IBTC mallakin kamfanin Multi-functions Nigeria Limited da kuma N800, 663.43 a bankin Citibank shima mallakin kamfanin.”Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel