Yansandan SARS sun kama wani mutumi saboda ya ajiye gemu, beli N50,000

Yansandan SARS sun kama wani mutumi saboda ya ajiye gemu, beli N50,000

Jami’an sashin yaki da yan fashi da makami na rundunar Yansandan Najeriya sun kama wani matashi mai suna Tochi Nwawuba da laifin ajiye gemu, har da kafta masa ankwa, har sai ya yi belin kansa a kan kudi N50,000.

Matashin Injiniyan da kansa ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Instagram, inda yace lamarin ya faru ne a unguwar Lekki phase 1 dake jahar Legas, inda yace Yansandan suka tare shi, sa’annan suka buga masa ankwa kawai saboda ya ajiye gemu mai yawa a fuskarsa.

KU KARANTA: Matashi ya tubure a kan N99,000 da aka aika masa bisa kuskure ta asusun bankinsa

Tochi yace da farko bayan sun kamashi sai suka sanya kudin belinsa a kan N200,000, amma daga karshe sai daya biya N50,000 suka sakeshi, duk da cewa ya nuna musu katin shaidar wurin aikinsa, watau I.D Card, amma suka yi biris da shi.

Ga dai jawabin Tochi kamar haka: “Jiya Yansandan SARS suka kamani a kan hanyata ta zuwa wurin aiki, gamuna ya zama matsalar Najeriya duk da cewa na fada musu ni Injiniya ne, kuma na nuna musu ID na, amma suka yi biris.

“Abinda suke so kawai shi ne na basu wayata da kwamfuta ta dake kujerar bayan motata, ni ma na ki ya, da haka suka kamani, suna neman na basu kudin beli N200,000 saboda bamu da yanci a kasar nan amma daga karshe sai da na biya N50,000 kudi hannu suka sake ni.

“Na biya kudin ne saboda sun ce za su iya harbeni, sa’annan su kala min sharrin aikata wani laifi idan har ban basu hadin kai ba.”

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira ga Yansandan Najeriya dasu kauce ma cin zarafin yan Najeriya da kuma kwatar kudi daga hannunsu, sai dai tamkar basu san ma yana yi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel