Buratai ya roki yan jarida da su daina bata sunan dakarun sojoji wadanda suka sadaukar da rayuwarsu don kare al’umma

Buratai ya roki yan jarida da su daina bata sunan dakarun sojoji wadanda suka sadaukar da rayuwarsu don kare al’umma

Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya roki yan jarida da su daina shafawa jami’an rundunar sojin Nasjeriya bakin fenti.

Buratai ya yi magana ne a wani taron kwanaki biyu na alaka tsakanin kafofin sadarwa da sojoji wanda yan jarida suka shirya a kudu maso gabas.

Shugaban sojojin ya zargi kafofin watsa labarai da yan jarida da fadin bakin rundunar sojin Najeriya fiye da alkhairinsu a gaban mabiyansu.

Buratai wanda ya samu wakilcin babban jami’in horarwa da ayyukan rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Eno Obong Udoh, ya bayyana cewa hukuma kamar irin ta rundunar sojin Najeriya ba za ta iya fitar da baragurbin kwai ba a cikin jami’anta.

Shugaban rundunar ya zargi kafofin watsa labarai da bata sunan jami’an sojojin wadanda ya ce suna sanya rayuwarsu a hatsari domin tabbatar da tsaron kasar.

KU KARANTA KUMA: Zargin karkatar da Biliyan 14 ta sa ana ce-ce-ku-ce tsakanin Majalisa da Minista

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta sayi sabbin motoci domin inganta aikin jami'an tsaron jihar musamman yanzu da sace-sace da garkuwa da mutane yayi tsamari.

Da safiyar Talata, 5 ga Nuwamba, gwamnan ya mikawa hukumomin tsaron sabbin motocin kirar 'Peugeot'.

Legit.ng Hausa ta samu labarin ne daga kwamishanan harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, inda ya bayyana hakan a shafin ra'ayi da sada zumunta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel