Na fuskanci wariyar launin fata a Bundesliga - Akpoborie

Na fuskanci wariyar launin fata a Bundesliga - Akpoborie

Tsohon dan wasan kwallon kafa na kasa da kasa, Jonathan Akpoborie, ya goyi bayan dan wasan kwallon kafa na kasar Italia, Mario Balotelli, akan yunkurin ficewa daga filin wasa sakamakon cin zarafinsa da aka yi akan launin fatarsa.

A wasan da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata tsakanin Brescia da Hellas Verona, Brescia ta samu wurga kwallo biyu cikin raga inda Hellas Verona ta samu wurga kwallo daya kacal.

Ya bayyana cewa, shi kanshi ya dinga samun irin wannan cin zarafin na wariyar launin fata lokacin da yake bugawa kasar Jamus kwallo.

DUBA WANNAN: Buhari na iya neman zarcewa kan mulki karo na uku - Buba Galadima

Tsohon dan kwallon kuma dan Najeriya, ya bugawa kungiyoyin kwallon kafa na kasar Jamus da suka hada da: Hansa Rostock, VfB Stuttgart da VfL Wolfsburg inda yaci kwallaye 143 a cikin wasa 325 da yayi a tarihin kwallon kafarsa.

"Wariyar launin fata na daga cikin abubuwa masu matukar bakin ciki a duniyar kwallon kafa. Na fuskanci wariyar launin fata a lokacin Bundeliga na," ya wallafa a shafinsa na twitter

A yayin maida martani akan hukuncin Balotelli na ficewa daga filin wasa, tsohon dan wasan ya bayyana cewa, lamarin wariyar launin fata yafi kuna ga wanda abin ya shafa,"

"Muna da halayya da dabi'u kala-kala. A don haka ne muke da hanyoyi daban-daban na yanke hukunci. Ba wanda zai fahimci yadda kaji, sai wanda aka taba yi wa hakan. Wariyar launin fata na daga cikin munanan abubuwan da zasu iya faruwa da dan adam."

Akpoborie ya ce, hukumomin kula da wasan kwallon kafa ne ya cancanta su yi wani abun azo a gani akan matsalar.

"Lokaci yayi da FIFA da UEFA zasu tashi tsaye. Akwai bukatar su dau abun ba da wasa ba. Za a iya hanawa," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel