Gwamnan jihar Kaduna ya siyawa jami'an tsaro sabbin motocin sintiri (Hotuna)

Gwamnan jihar Kaduna ya siyawa jami'an tsaro sabbin motocin sintiri (Hotuna)

Gwamnatin jihar Kaduna ta sayi sabbin motoci domin inganta aikin jami'an tsaron jihar musamman yanzu da sace-sace da garkuwa da mutane yayi tsamari.

Da safiyar Talata, 5 ga Nuwamba, gwamnan ya mikawa hukumomin tsaron sabbin motocin kirar 'Peugeot'.

Legit.ng Hausa ta samu labarin ne daga kwamishanan harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, inda ya bayyana hakan a shafin ra'ayi da sada zumunta.

Yace: "Da safiyar nan, gwamna Nasir El-Rufa'i a madadin gwamnatin jihar Kaduna ya gabatar da motoci ga hukumomin tsaron dake aiki a jihar Kaduna."

"An yi domin inganta hukumomin tsaro da ingancin sintirinsu."

Gwamnan jihar Kaduna ya siyawa jami'an tsaro sabbin motocin sintiri (Hotuna)

Gwamnan jihar Kaduna ya siyawa jami'an tsaro sabbin motocin sintiri (Hotuna)
Source: Facebook

A ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba, Wasu al’ummar unguwar Rigasa ta jahar Kaduna sun gudanar da zanga zangar lumana a gaban majalisar dokokin jahar Kaduna inda suka koka kan yawaitan satar mutane tare da garkuwa dasu da ake samu a yankin.

Sun nemi majalisar dokokin jahar Kaduna ta shiga cikin maganan domin kawo musu dauki a halin da suke ciki, sa’annan sun yi kira ga majalisar da ta sanya baki wajen ganin an canza Yansandan dake Rigasa gaba daya.

KU KARANTA: Ofishin mataimakin shugaban kasa ke mini bita da kulli saboda biyayya na gareka - Obono-Obla ya kaiwa Buhari kuka

Masu zanga zangar sun isa majalisar ne da misalin karfe 11 na safiyar Litinin, jim kadan bayan kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya gabatar kasafin kudin ma’aikatarsa na shekarar 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel