Zargin karkatar da Biliyan 14 ta sa ana ce-ce-ku-ce tsakanin Majalisa da Minista

Zargin karkatar da Biliyan 14 ta sa ana ce-ce-ku-ce tsakanin Majalisa da Minista

Ministan kasuwanci da zuba jari, Niyi Adebayo, ya fada ma kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kudi cewa ba a tura kowani naira biliyan 14 zuwa wani kamfani mai zaman kansa ba.

Kwamitin majalisar dattawa kan kasuwanci da zuba jari ya gayyace shi kan zargin ma’aikatar da tura kudi har naira biliyan 14 zuwa wani kamfani mai zaman kansa a matsayin kasafin kudi.

Ministan, wanda ya gurfana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kudi, yace har yanzu kudin na a karkashin kulawar babban bankin Najeriya.

Ya ce kamfanin da ake zargin an turawa kudin ya kasance mallakar gwamnatin tarayya ne.

Ya ce ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari ce ta kafa kamfanin tare da hadin gwiwar masu zuba jari masu zaman kansu wanda ma’aikatar ta gayyata, inda ma’aikatar ke da jari mafi girma a kamfanin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta gindaya sharudan bude iyakokin Najeriya

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kudi, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa majalisar ba za ta samar da komai ga ma’aikatar ba har sai an magance lamarin.

Ma’aikatar ta gabatar da N8,988,010,031,00 na kasafinta inda kwamitin kasafin kudi ya ki amincewa dashi har zuwa lokacin da za a magance lamarin naira biliyan 14 da aka amince mata a kasafin kudin 2018.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel