Kungiyar 'yan kasuwar Ghana ta kara garkame shaguna 50 na 'yan Najeriya a kasar

Kungiyar 'yan kasuwar Ghana ta kara garkame shaguna 50 na 'yan Najeriya a kasar

A jiya Litinin ne kungiyar masu siyar da kayan wutar lantarki ta kasar Ghana ta garkame shagunan bakin haure, ganin cewa sun take dokar kasar.

A kalla shaguna 50 na 'yan Najeriya aka garkame a Opera Square da ke tsakiyar Accra, babban birnin kasar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayar da rahoto.

A makon da ya gabata ne kungiyar ta ba masu shaguna da ba 'yan kasar ba wa'adin rufe shagunansu zuwa watan Nuwamba.

Mai magana da yawun kungiyar, Samuel Addo, ya ce, hakan ya yi dai-dai da tanadin doka ta sashi na 27, sakin layi na 1 a dokokin hukumar habaka hannayen jari ta Ghana.

DUBA WANNAN: Buhari na iya neman zarcewa kan mulki karo na uku - Buba Galadima

Da karfe 10 na safe ne 'yan kungiyar suka isa shagunan 'yan Najeriya da ke rukunin wajen kasuwancin tare da umartarsu da barin shagunan inda suka garkame shagunan da kwado.

'Yan kasuwar Ghana basu wani samu matsala ba saboda 'yan Najeriyan sunyi biyayya hadi da cewa babu jami'an tsaro a wurin.

Wasu 'yan Najeriya da suke ganin sun zama 'yan kasar saboda a nan aka haifesu ko auratayya sun roki masu masaukin nasu da kada su garkame musu shagunansu.

Shugaban kungiyar 'yan kasuwar Najeriya da ke Ghana, wanda a gabanshi lamarin ya faru ya mika kokensu ga 'yan sanda.

An samu natsuwa a Opera Square da yammacin jiya yayin da aka cigaba da gudanar da kasuwanci ba tare da wata matsala ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel