Ribadu: Tun da Buhari ya zama Ministan mai, babu wanda ya mallaki Biliyoyi

Ribadu: Tun da Buhari ya zama Ministan mai, babu wanda ya mallaki Biliyoyi

Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa na farko, Nuhu Ribadu, ya ce babu wanda ya zama Biloniya a zamanin shugaba Muhammaud Buhari.

Malam Nuhu Ribadu da ya ke yi wa wasu sababbin Kwamishinoni bita, ya ce tun da shugaban kasar ya karbi kujerar Ministan man fetur, babu wani mahalukin da ya samu kazaman kudi.

The Cabe ta ce Malam Ribadu ya yi jawabin nan ne Ranar 4 ga Watan Nuwamba, 2019, a garin Gombe sa’ilin da ya ke magana a kan yaki da cin hanci rashawa da satar dukiyar gwamnati.

Gwamnatin jihar Gombe ta shirya wannan zama na wayar da kai ne ga Kwamishinonin da za su shiga ofis da kuma Hadiman da ke ba gwamnan jihar shawara da kuma Sakatarorin din-din-din.

KU KARANTA: Tsohon Hadimin Buhari ya zargi Osinbajo da shirya masa mugun nufi

Tsohon shugaban na EFCC ya bayyana cewa an yi maganin satar dukiyar kasa a bangaren man fetur a gwamnatin Buhari. Ribadu ya nemi jami’an gwamnatin Gombe su yi irin wannan aniya.

“Tun da shugaba Muhammadu Buhari ya zama Ministan man fetur, ban ga mutane su na zama Biloniyoyi daga harkar man fetur ba, saboda an samu shugaba wanda bai satar kudin kasa.”

Ribadu ya kuma yi kira ga wadanda su ka samu mukamin da su guji afkawa taba baitul-mali. “Ka da ku sake ku yi zamiya, hukumomin EFCC da NFIU su na ganinku, kuma su na iya kama ku.”

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya yi jawabi a wajen wannan muhimmin taro da aka shirya. SGF din ya yi kira ga gwamnatin Gombe ta yi aiki da Sarakuna wajen tafiyar da mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel