Kogi: Zan bankado dukkan badakalar da gwamnatin Bello ta yi idan aka zabe ni - Wada

Kogi: Zan bankado dukkan badakalar da gwamnatin Bello ta yi idan aka zabe ni - Wada

Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kogi, Musa Wada ya ce zai binciki gwamnatin Gwamna Yahaya Bello idan aka zabe shi yayin zaben ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar.

Wada ya ce ba zai yi a kasa a gwiwa ba wurin bankado badakalar da ake gudanarwa a jihar a halin yanzu kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya ce tsoron irin wannan binciken ne yasa gwamnatin mai ci yanzu ta tayar da hankalinta wurin ganin ta cigaba da kasancewa kan mulki don ta cigaba da cin zalin al'ummar jihar.

A jawabin da ya yi a ranar Lahadi, Wada ya ce zai binciki dukkan ayyukan da aka gudanar cikin shekaru hudu na mulkin Gwamna Yahaya Bello a jihar.

DUBA WANNAN: Buhari na iya neman zarcewa kan mulki karo na uku - Buba Galadima

Ya shawarci al'ummar jihar su yi amfani da kuri'unsu su hambarar da gwamnatin mai ci yanzu da ke amfani da jam'iyyar APC tana damfarar su.

A cewarsa: "Babu wani kwaskwarima da za a iya wa haram, an yaudari mutane an biya wasu ma'aikatan gwamnati albashi an bar wasu da ke bin bashin albashin fiye da watanni 40 duk saboda an ga zabe ya matso. Ya ce abinda ya fi wannan muni zai faru idan har aka sake zaben APC.

"Abinda na sani shine, zan binciki dukkan abinda aka gudanar cikin shekaru hudu na mulkin Gwamna Yahaya Bello da 'yan korarsa, a shirye na ki don in bankado duk wata badakalla da gwamnatin baya ta aikata."

Dan takarar na PDP ya kuma gargadi kungiyar kwadago da kada su yarda gwamnatin da tursasa musu daukan matakan da ba zai amfani ma'aikatan jihar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel