Ofishin mataimakin shugaban kasa ke mini bita da kulli saboda biyayya na gareka - Obono-Obla ya kaiwa Buhari kuka

Ofishin mataimakin shugaban kasa ke mini bita da kulli saboda biyayya na gareka - Obono-Obla ya kaiwa Buhari kuka

Tsohon Shugaban kwamitin bincike da kwato kudin sata SPIP, Okoi Obono-Obla, ya bayyana cewa ofishin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, na yi mas abita da kulli ne saboda biyayyarsa ga shugaba Buhari.

An kafa kwamitin SPIP ne domin binciken rashawa da satan ma'aikatan gwamnati ke yi.

A wasikar da ya turawa shugaba Buhari, Okoi Obono-Obla ya ce wasu kusoshi a ofishin mataimakin shugaban kasa ya bukaci su hada baki domin karbar cin hanci kan wani bincike amma ya kiya.

Ya ce ana yi masa bita da kulli ne saboda biyayyar da yake yiwa shugaba Buhari da kuma kin biyayya ga mataimakinsa dake bukatarsa ya yi ha'inci.

DUBA WANNAN An bankado gidan ajiye kangararru a Ibadan, an ceto 400

Yace: "An kafa kwamitin ne lokacin da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ke mukaddashin shugaban kasa. Ya nada daya daga cikin hadimansa, Adeniran Gbolahan, matsayin sakataren kwamitin."

"Daga baya na samu matsala da shi kan shin ta wani dalili kwamitin za ta rika jiran umurni daga mataimakin shugaban kasa kafin ta kaddamar da wani bincike."

"Amma sakataren ya samu goyon bayan mataimakin shugabann kasa ta hannun mataimakin shugaban ma'aikatan Osinbajo, Mista Ade Ipaye, domin cin mutuncina."

Obono-Obla ya kara da cewa ofishin mataimakin shugaban kasa ta hana shi gudanar da bincike kan wasu zarge-zargen rashawa kan wasu yan majalisar dokokin tarayya.

A ranar 22 ga Oktoba, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC ta alanta neman Okoi Obono-Obla ruwa a Jallo.

Hukumar ta bayyana cewa ta dau wannan mataki ne saboda Obono-Obla ya ki bayyana gabanta duk da sammacin da tayi masa domin amsa tambayoyi bisa ga zargin da ake yi masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel