Kuma dai: An bankado gidan ajiye kangararru a Ibadan, an ceto 400

Kuma dai: An bankado gidan ajiye kangararru a Ibadan, an ceto 400

Hukumar yan sanda a jihar Oyo, a ranar Litinin, ta ceto mutane 400 da aka tsare a wani gidan gyaran kangararru dake cikin Masallaci a unguwar Ojoo na garin Ibadan, birnin jihar Oyo.

Kwamishanan yan sandan jihar, Shina Olukolu, wanda ya jagoranci yan sandan zuwa wajen ya ce wani dan shekara 17 da ya tsira daga wajen ne ya tuntunbi yan sanda.

A cewarsa, sun garzaya Masallacin kuma suka tarar da matasa cikin mari, maza, mata da yara. Wasu daga cikinsu sun laburta cewa sun kwashe shekaru da dama a tsare.

Kwamishanan yace: "Da yan sanda suka isa wajen, mun ga matasa maza da mata da ake tsarewa a wajen tamkar kurkuku. Hakika dan Adam na zaluntan dan Adam irinsa, wannan shine siffar abun. Kuma gaskiya abin bai yi mana dadi ba."

"Sai muka tuntubi gwamnatin jihar kuma jami'an gwamnatin suka iso. Sun zo domin tabbatar da cewa wadannan matasa sun koma gida kuma zasu iya kula da kansu."

"Ko shakka babu, zamu kiyaye wannan waje kuma hukumar yan sanda za ta zurfafa bincike, kuma duka wanda aka kama da hannu cikin wannan abu, zamu damkeshi da hukuntashi saboda hakan ya zama izina ga wasu masu irin haka."

Wannan shine karo na farko da za'a bankado irin wadannan gidajen ladabtar da kangararuu a kudancin Najeriya.

A makonnin baya, an kasance ana bankado irin wadannan gidaje a Arewacin Najeriya musamman a jihar Kaduna, Kano, Katsina, Kwara da Adamawa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel