“A daina boye shinkafa, mu na da abin da za mu ci na shekara biyu”

“A daina boye shinkafa, mu na da abin da za mu ci na shekara biyu”

Wani babban Manomin shinkafa a jihar Enugu, Ekene Uzodinma, ya yi kira ga mutanen Najeriya da su daina sayen shinkafa su na boyewa yayin da ake shirin dumfarar bukuwan Kirismeti.

Mista Ekene Uzodinma ya yi wannan kira ne a lokacin da ya yi wata hira da hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN a Ranar Litinin, 4 ga Watan Nuwamba, 2019, inda ya bada shawarwari.

Uzodinma wanda shi ne shugaban kamfanin noman Excellent Integrated Ltd, ya bayyana cewa akwai shinkafar da za su isa ayi shekaru kusan biyu ana ci a Najeriya ba tare da an nemi kari ba.

Babban Manomin kasar ya fadakar da jama’a cewa yawan sayen shinkafan fiye da bukata ne zai jawo farashi ya tashi. Uzodinma ya ce tun farko babu dalilin a rika sayen buhuna domin a boye.

KU KARANTA: Mutane 1000 za a dauka aiki a kamfanin kayan gonan Obasanjo

“Ana yaudarar wasu ‘Yan Najeriya a kafafen sadarwa na zamani cewa rufe iyakoki zai sa shinkafa ta yi karanci kuma farashi ya tashi. Amma wannan kanzon-kurege ne domin akwai shinkafa.”

“Ina nufin mu na da shinkafar gida wanda za ta isa Najeriya shekaru biyu ana ci. Sai ka ga gidan da ake bukatar buhu guda, su na sayen buhuna goma ko fiye na shinkafa a lokaci guda.” Inji sa.

Manomin da ya yi kaurin suna wajen noman shinkafa ya ce: “Akwai wadanda su ka yi amfani da rufe iyakokin da aka yi wajen boye shinkafa domin su fito su saida a daidai lokutan bukukuwa.”

“Amma idan jama’a su ka saye shinkafa a hankali, babu abin da zai fa farashin ya tashi sama, kuma buhunan shinkafar da mu ke da su, sun ishe mu gaba daya.” Uzodinma ya kare jawabinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel