Matashi ya tubure a kan N99,000 da aka aika masa bisa kuskure ta asusun bankinsa

Matashi ya tubure a kan N99,000 da aka aika masa bisa kuskure ta asusun bankinsa

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta samu nasara a gaban kotu a kan wani matashi mai suna Orhena Bartholomew wanda ya cinye N99,000 da aka aika masa bisa kuskure ta asusun bankinsa.

Rahoton jaridar Premium Times ta ruwaito Alkalin babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Makurdi, mai sharia Mobolaji Olajuwon ne ya yanke ma Orhena hukuncin daurin shekaru 2 a kurkuku ko kuma biyan taran N50,000.

KU KARANTA: Majalisar dokokin jahar Kano ta tsayar da ranar tantance sabbin kwamishinoni 20

Majiyar Legit.ng ta ruwaito rikicin ya samo asali ne a lokacin da wani Orhena ya tafi wajen mutumi dake sana’ar tura kudi ta tsarin First Monie Cash Point domin ya tura ma wani abokinsa N1,000 a asusun bankinsa, inda ya mika ma mutumin N1,000 a hannu.

Sai a bisa kuskure irin na dan Adam, sai mutumin ya tura ma abokin Orhena N100,000, koda mutumin ya nemi Orhena ya yi ma abokinsa magana su dawo masa da N99,000, sai Orhena yace ai tuni ya na kan hanyar zuwa Legas, kuma ba zai dawo ba.

Ashe shi wancan abokin Orhena ya ga wadannan kudade, don haka sai ya mayar ma Orhena duka N99,000 ba tare da ko kwabo ya yi ciwon kai ba, amma sai Orhena ya ki mayar ma mai kudin, ya tafi ya sayi babur kirar Honda.

Daga bisani ne mutumin ya kai karar Orhena ga hukumar EFCC, inda ta samu nasarar kama shi, har ta gurfanar da shi gaban kotu, sai dai Orhena bai baiwa shari’a wahala ba, inda ya amsa laifinsa.

Daga karshe EFCC ta tilasta ma Orhena yin kashin N99,000 daya cinye tun a lokacin da take gudanar da bincike a kansa, sa’annan ta kwace babur din daya saya, kuma ta mika ta ga gwamnatin tarayya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel