Tsohon sanata ya maka hukumar 'yan sanda kotu akan kisan danshi, ya bukaci diyya

Tsohon sanata ya maka hukumar 'yan sanda kotu akan kisan danshi, ya bukaci diyya

Wani tsohon dan majalisa, Sanata Fidelis Okoro, ya maka hukumar 'yan sandan Najeriya a kotu tare da wasu mutane biyu akan zargin kashe dansa da wani jami'in 'yan sanda yayi.

Ya zargi cewa dansa, John Chukwuemeka Okoro mai shekaru 31, wanda ya kammala karatunsa a fannin kasuwanci a wata jami'a dake Landan, ya rasa ransa ne sakamakon harbinsa a kafa da kirji da wani dan sanda yayi. Mohammed Yusuf, mai mukamin ASP a hukumar ya harbi dansa a kafa da kirji ne a ranar 11 ga watan Augusta na shekarar 2014 yayin da suke hutawa tare da abokinsa a yankin Gudu dake Abuja.

An gano cewa, 'yan sandan suna neman wasu masu satar mota ne.

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi talauci a Najeriya

A karar da lauyan tsohon sanatan ya shigar, J. K Mbanefo Ikwegbue Esq, Sanata Okoro, wanda ya taba wakiltar yankin Enugu ta raewa tsakanin 1999 da 2007, yana bukatar diiyar naira biliyan 3 a matsayin kudin fansa da kuma kisan ba gaira ba dalili da aka yiwa dansa.

Sanata Okoro, wanda ya hada da hukumar 'yan sanda, sifeta janar din 'yan sanda tare da ASP Yusuf a kararsa, ya jaddada cewa, bayan binciken da hukumar 'yan sandan tayi akan lamarin, bata dau wani kwakwaran mataki akai ba.

Ya kara da cewa, rasa dansa da yayi da kuma yanda hukumar 'yan sanda ta dau lamarin ya jawo mishi tsananin rashin natsuwa da rashin lafiya.

Jastis Inyang Ekwo ya dage shari'ar karar zuwa ranar 5 ga watan Disamba don cigaba da sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel