An halaka daliban jami’a 13 a rikicin kungiyoyin asiri a jahar Kogi

An halaka daliban jami’a 13 a rikicin kungiyoyin asiri a jahar Kogi

Matasa yan kungiyoyin asiri dauke da muggan makamai sun far ma junansu a jami’ar jahar Kogi dake garin Ayingba, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar dalibai 13, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Rahotanni sun bayyana lamarin mai muni ya auku ne a ranar Juma’ar data gabata, sai dai silar rikicin an bayyana shi ne kisan wani jagoran yan kungiyar asiri a kwalejin kimiyya da fasaha dake garin Lokoja, inda ake zargin wata kungiyar asiri dake jami’ar Ayingba ne suka kashe shi.

KU KARANTA: Majalisar dokokin jahar Kano ta tsayar da ranar tantance sabbin kwamishinoni 20

Kisan wannan jagora ne yasa yaransa dake kwalejin kimiyya da fasaha na Lokoja suka taru, suka kaddamar da hari a jami’ar KSU domin daukan fansa, inda suka kashe dalibai 13 a zuwa daya.

Haka zalika rahotannin sun tabbatar da cewa daliban jami’ar guda uku kadai aka kashe a cikin jami’ar, yayin da sauran mamatan an bi su har gidajen da suke zama ne a cikin garin Ayingba aka halakasu.

Daga cikin wuraren da aka kashe daliban akwai layin Stadium da kuma gidan saukan baki na Our Lady Fatima. Sai dai koda majiyarmu ta tuntubi mai magana da yawun jami’ar, Joseph Edegbo don jin ta bakinsa, sai ya ki amincewa ya yi magana saboda girman lamarin.

A nata bangaren kuwa, rundunar Yansandan jahar Kogi, ta bakin kwamishinan Yansandan Kogi, Hakeem Busari ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace dalibai 3 kadai aka kashe, sa’annan yace basu kama kowa ba har yanzu, amma jami’ai na cigaba da farautar duk masu hannu cikin kashe kashen.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa satar mutane da garkuwa dasu ba zai kare a Najeriya ba sakamakon ya zama hanyar samun kudi ga wasu tsirarun miyagun mutane.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba a fadar gwamnatin jahar dake Fatakwal yayin daya karbi bakuncin kungiyar Rotary International District 1941, inda yace sai dai kawai a yi abinda za’a iya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel