Neja-Delta: Sanata ya yi zaune a kan kwangiloli 300, an biya kudi kuma bai yi aikin ba – NDDC

Neja-Delta: Sanata ya yi zaune a kan kwangiloli 300, an biya kudi kuma bai yi aikin ba – NDDC

Cairo Ojougboh, wanda Darektan rikon kwarya ne na ayyuka a hukumar NDDC mai kula da cigaban Neja-Delta, ya bayyana cewa akwai Sanatan Najeriyan da aka ba kwangiloli 300 a yankin.

Ojougboh, wanda bai kama sunan Sanatan ba, ya tabbatar da cewa an biya sa akalla kudin kwangila 120. Yanzu haka ana binciken duk kwangiloli da aka bada da kuma halin da su ke ciki.

Mista Ojougboh ya yi wannan bayani ne a babban birnin tarayya Abuja lokacin da ya yi wata zantawa da Manema labarai. A wajen wannan zama ne ya ce NDDC ta na bin bashin Tiriliyan uku.

Darektan na NDDC ya ke cewa binciken kwa-kwaf din da za ayi, zai taimakawa hukumar wajen duba yadda ta tara wadannan bashin kwangiloli don haka ya nemi jama'a su bada hadin-kai.

KU KARANTA: Ba za a fasa binciken Hukumar NNDC ba - Minista

Yanzu dai shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti na mutum uku da za su bi diddikin abubuwan da su ka faru a hukumar NDDC tun daga shekarar 2001 har zuwa shekarar nan ta 2019.

Wani mai neman babban kwangila a NDDC, kuma ya na cikin ‘yan majalisar dattawa ya na da ayyuka 300 a NDDC shi kadai. Daga ciki an biya sa kudin ayyuka 120 cir, amma bai yi aikin ba.”

“Satifiket din kwangila da aka yanka ya haura na Tiriliyan uku. Wannan shi ne abin da NDDC ta ke bin bashi wajen wadannan gawurtattun ‘yan kwangila. Shiyasa su ke kiran a daina binciken.”

“Abin da ya sa ya ke yin wannan shi ne saboda ta’adin da ake yi a NDDC ya cigaba kuma wannan shi ne abin da kwamitin da aka kafa ba za ta bari ba. Iyakar ta kenen kawai.” Inji C. Ojougboh.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel