Kulle boda: Farashin shinkafa zai fadi warwas kafin karshen shekara – Gwamna Bagudu

Kulle boda: Farashin shinkafa zai fadi warwas kafin karshen shekara – Gwamna Bagudu

Majalisar tabbatar da abinci a Najeriya, NFSC, dake karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa farashin shinkafar gida zai karye warwas kafin bikin kirismeti dake zuwa a karshen shekara.

Mataimakin majalisar, kuma gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labaru a lokacin ziyarar daya kai kasar Saudiyya tare da shugaba Buhari, inda yace suna sane da tashin gwauron zabi da farashin shinkafar ta yi.

KU KARANTA: Majalisar dokokin jahar Kano ta tsayar da ranar tantance sabbin kwamishinoni 20

“Farin cikinmu shi ne ana ta noman shinkafa, kamfanonin cashe shinkafa suna samun isashshen shinkafa, ga kuma za’a fara girbi nan bada jimawa ba, kuma zamu tabbata mun kai shinkafa zuwa kasuwannin da ake ganin za’a samu karancinta.

“Muna sane da mutanen dake kokarin yin amfani da wannan dama domin samun kazamar riba, kokarinsu shi ne su lalata tsare tsaren gwamnati game da tattalin arziki, kuma zamu dauki matakin daya dace a kansu.” Inji shi.

Da yake tsokaci game da ikirarin tafka asarar naira biliyan 1 da manoman albasa suka ce sun yi, Bagudu yace gwamnati za ta dauki matakin daya kamata game da hakan, amma yace duk dai basu tabbatar da adadin asarar ba, amma suna sane da cewa yawan ruwan sama da aka samu har bayan watan Satumba ne ya janyo ma manoman albasa asara.

Idan za’a tuna tun bayan garkame iyakokin Najeriya da makwabtanta ne farashin shinkafa mai nauyin kilo 50 ya tashi daga N14,000 zuwa N22,000, sakamakon haramta shigoda ita da gwamnati ta yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel