El-Rufa'i zai gina gidaje na biliyan N3 domin masu karamin samu

El-Rufa'i zai gina gidaje na biliyan N3 domin masu karamin samu

Gwamnatin jihar Kaduna ta ware biliyan N3 domin gina gidaje da masu karamin karfi zasu iya mallaka a cikin shekarar 2020, kamar yadda kwamishinar gidaje da raya karkara ta jihar Kaduna, Fausat Ibikunle, ta bayyana.

Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne yayin da take kasafin kudin ma'aikatarta a gaban majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Litinin.

A cewar ta, ma'aikatar ta ware fiye da biliyan N9 domin gudanar da manyan aiyuka, yayin da ta ware miliyan N74 domin harkokin gudanar wa.

"Muna fatan fara gina gidaje a marayu domin masu karamin karfi kafin karshen shekarar 2020," a cewar ta.

Ta kara da cewa za a kashe biliyan N3 wajen gina gidaje da masu karamin karfi zasu iya mallaka, sannan a kashe wata biliyan guda domin tsarin asusun gata na musamman.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin karkara da gidaje, Ahaji Yusuf Salihu, ya ce suna fatan cewa sabuwar ma'aikatar zata saukaka wa masu karamin karfe rayuwa.

DUBA WANNAN: Kaduna: El-Rufai ya bayar da umarnin a biya sabbin ma'aikata dukkan bashin da suke bin gwamnati

A baya Legit.ng ta wallafa labarin cewa kotun daukaka kara dake zamanta a Kaduna ta tsayar da ranar 7 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da zata yanke hukunci a kan karar da jam'iyyar PDP da dan takararta na gwamna a jihar Kaduna, Alhaji Isa Ashiru, suka daukaka a kan zaben ranar 9 ga watan Maris, 2019.

Ashiru da jam'iyyar PDP sun garzaya kotun daukaka karar ne bayan kotun sauraron korafin zabe ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya samu a zaben gwamnan jihar Kaduna.

Kotun a karkashin mai shari'a Jatis Ibrahim Bako ta kori karar da jam'iyyar PDP da dan takararta suka shigar bisa hujjar cewa bata cika ka'idoji ba.

Masu kara sun gabatar da shaidu 135 a gaban kotun da tarin wasu takardu domin tabbatar da zargin da suke yi a kan cewa an tafka magudi a zaben da aka gudanar. Kazalika, sun yi zargin cewa an yi cushen kuri'u a akwatunan zabe tare da yin amfani da 'yan daba domin kawo tsaiko yayin kada kuri'u.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel