Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Rann

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Rann

Yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun kai hari kauyen Rann, karamar hukumar Kala Balge ta jihar Borno inda suka hallaka manoma uku, kuma sukayi waon gaba da mata 6, Daily Nigerian ta bada rahoto.

An samu rahoton cewa yan ta'addan sun dira kauyen ne ranar Lahadi suna harbin kan mai uwa da wabi.

Wani majiya da aka sakaye sunansa ya bayyana cewa: "Yawancin wadanda harin ya shafa manoma be. Yan Boko Haram sun kashe uku kuma sun sace mata shida."

Zainab Gimba, wata yar majalisar dokokin jihar mai wakiltar Bama, Ngala da Kala Balge, ta tabbatar da harin ga manema labarai.

Tace: "Boko Haram sun sace mata kuma sun kashe manoma a mazabata. Wani mazauni ya kawo min labarin abinda ya faru ranar Lahadi a wayar tarho da lambar Kamaru."

Har yanzu hukumar Sojin Najeriya ba tayi tsokaci kan wannan hari ba.

KU KARANTA: Tsawon shekaru 40 kasar Sin ta rufe iyakokinta, gashi yau sai gaskiya - Hamid Ali

Kauyen Rann ta shahara da kisan mutane da Boko Haram ke yi tun lokacin da aka fara wannan yakin.

A ranar 17 ga Junairun 2017, jami'ar hukumar sojin sama sun yi kuskuren ruwan bama-bamai kan sansanin yan gudun Hijra a Rann inda akalla mutane 52 suka hallaka kuma daruruwa suka jikkata.

Hakazalika a watan Junairun 2019, yan Boko Haram sun kai hari sansanin yan gudun hijran kuma suka hallaka akalla mutane 60, a cewar rahoton Amnesty International.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel