Majalisar dokokin jahar Kano ta tsayar da ranar tantance sabbin kwamishinoni 20

Majalisar dokokin jahar Kano ta tsayar da ranar tantance sabbin kwamishinoni 20

Majalisar dokokin jahar Kano ta tsayar da ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba domin fara tantance mutanen da gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya aika mata da sunayensu da yake muradin nadasu mukamin kwamishinoni.

Kaakakin majalisar dokokin jahar Kano, Garba Gafasa ne ya bayyana haka bayan ya karanta ma takwarosinsa wasikar da gwamnan ya aiko ma majalisar dake kunshe da sunayen sabbin kwamishinonin, inda ya nemi mutanen su so da yan rakiya mutum biyu kacal.

KU KARANTA: Jama’an Kaduna sun fusata, sun yi ma majalisa dokoki tsinke a kan garkuwa da mutane

A ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba ne gwamnan Kano ya aika ma majalisar da sunayen sabbin kwamishinonin nasa su 20, daga cikinsu akwai sabbin fuskoki guda 12, sai kuma tsofaffin fuskoki guda 8.

Tsofaffin kwamishinonin da gwamnan ya sake aika sunansu ga majalisa sun hada da kwamishinan watsa labaru Muhammad Garba, kwamishinan kananan hukumomi Muratala Sule-Garo, Musa Iliyasu Kwankwaso, Ibrahim Mukhtar, Kabiru Ibrahim Getso, Shehu Na-Allah Kura, Mukhtar Ishaq da Muhammad Tahir Adam.

Yayin da sabbin fuskokin suka hada da Ma’azu Magaji, Nura Muhammad-Dankade, Zahra’u Umar-Muhammad, Aminu Ibrahim-Tsanyawa, Sadiq Aminu-Wali, Muhammad Baffa-Takai da Kabiru Ado-Lakwaya.

Sauran kuma sune: ariya Mahmoud-Bunkure, Ibrahim Ahmad-Karaye, Mahmoud Muhammad-Dansantsi, Muhammad Sanusi-Sa’id da Lawan Abdullahi-Musa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel