Tsawon shekaru 40 kasar Sin ta rufe iyakokinta, gashi yau sai gaskiya - Hamid Ali

Tsawon shekaru 40 kasar Sin ta rufe iyakokinta, gashi yau sai gaskiya - Hamid Ali

Kwantrola Janar na hukumar hana fasa kwabrin, Kanar Hamid Ali, ya ce rufe iyakokin Najeriya da akayi zai yi matukar taimakawa cigaban kasar.

Yace: "Wannan gwamnati ce wacce ta lashi takobin cewa wajibi ne mu gina Najeriya, mu ci kayan noman Najeriya."

"Kasar Sin da muke zuwa siyo kusan dukkan kayayyakin da muke amfani da su, shin kun san shekaru nawa suka rufe iyakokinsu? Sun rufe iyakokinsu na tsawon shekaru 40 kuma gashi yau sun girma. Shin baku son Najeriya ta girma ne?"

Hamid Ali ya yi watsi da maganar da mutane ke yi cewa rufe boda ya tsananta halin yunwa da kuncin da yan Najeriya ke ciki.

Yace: "Tunanin cewa rufe boda ne ya janyo halin kuncin da yan Njeriya suke ciki karya ne. Kafin yau munada talakawa. Kafin yau munada mutanen da basu iya samun abinci sau uku a rana."

"Babu wani hujja kan haka. Wannan rufe iyakokin alkahiri ne ga Najeriya. Bari in fada muku dalili, ku ba manoma bane. Ku je Abakaliki ku tattauna da manoma, kuje Kebbi ku tattauna da manoma."

KO KA SAN Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Rann

Shugaba Hukumar DSS, Magaji Bichi, ya ce rufe iyakokin da Najeriya da gwamnatin tarayya tayi ya taimaka wajen rage fataucin makamai kuma ya taimakawa jami'an tsaro wajen lura da shiga da ficen mutanen da ka iya zama kalubale ga zaman lafiyar kasa.

Mista Bichi ya bayyana hakan ne a taron yaye daliban ilimin leken asiri da Abuja.

Ya roki gwamnati ta sanyawa iyakokin katangar karfe har sai lokacin da abubuwa suka daidaita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel