An zo wurin: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan karar da PDP ta daukaka a kan El-Rufa'i

An zo wurin: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan karar da PDP ta daukaka a kan El-Rufa'i

Kotun daukaka kara dake zamanta a Kaduna ta tsayar da ranar 7 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da zata yanke hukunci a kan karar da jam'iyyar PDP da dan takararta na gwamna a jihar Kaduna, Alhaji Isa Ashiru, suka daukaka a kan zaben ranar 9 ga watan Maris, 2019.

Ashiru da jam'iyyar PDP sun garzaya kotun daukaka karar ne bayan kotun sauraron korafin zabe ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya samu a zaben gwamnan jihar Kaduna.

Kotun a karkashin mai shari'a Jatis Ibrahim Bako ta kori karar da jam'iyyar PDP da dan takararta suka shigar bisa hujjar cewa bata cika ka'idoji ba.

Masu kara sun gabatar da shaidu 135 a gaban kotun da tarin wasu takardu domin tabbatar da zargin da suke yi a kan cewa an tafka magudi a zaben da aka gudanar. Kazalika, sun yi zargin cewa an yi cushen kuri'u a akwatunan zabe tare da yin amfani da 'yan daba domin kawo tsaiko yayin kada kuri'u.

DUBA WANNAN: Zamfara: Kotu ta tabbatar wa matawalle kujerarsa, ta ci tarar masu kara

Yayin zaman kotun daukaka karar mai alkalai biyar a ranar Litinin, babban alkalin kotun, Jastis U. I Anyawu, ya tsayar da ranar 7 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci bayan masu kara da wadanda ake kara sun kammala gabatar da shaidunsu da hujjojinsu.

A jawabin da lauyan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Dakta Nasiru Aliyu, da kuma lauyan gwamna El-Rufa'i, Abdulhakeem Mustafa (SAN), da kuma na jam'iyyar APC, Ibrahim K. Bawa, sun bukaci kotun daukaka karar ta yi watsi da bukatar Ashiru da jam'iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel