Jama’an Kaduna sun fusata, sun yi ma majalisa dokoki tsinke a kan garkuwa da mutane

Jama’an Kaduna sun fusata, sun yi ma majalisa dokoki tsinke a kan garkuwa da mutane

Wasu al’ummar unguwar Rigasa ta jahar Kaduna sun gudanar da zanga zangar lumana a gaban majalisar dokokin jahar Kaduna a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba inda suka koka kan yawaitan satar mutane tare da garkuwa dasu da ake samu a yankin.

Daily Trust ta ruwaito jama’a sun nemi majalisar dokokin jahar Kaduna ta shiga cikin maganan domin kawo musu dauki a halin da suke ciki, sa’annan sun yi kira ga majalisar da ta sanya baki wajen ganin an canza Yansandan dake Rigasa gaba daya.

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun kona barayin wayar salula 2 kurmus a jahar Delta

Masu zanga zangar sun isa majalisar ne da misalin karfe 11 na safiyar Litinin, jim kadan bayan kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya gabatar kasafin kudin ma’aikatarsa na shekarar 2020.

Da fari dai masu zanga zangar a karkashin jagorancin Barista Sani Shehu Sunusi sun yi kokarin kutsawa cikin majalisar, amma jami’an tsaro suka dakatar dasu. Guda daga cikinsu, Ismail Ahmad ya bayyana cewa a yanzu haka akwai mutane 50 har da mace mai juna biyu dake hannun yan bindiga.

A wani labarin kuma, mataimakin masu rinjaye na majalisar dokokin jahar Kaduna, Shehu Yunusa Pambeguwa ya shaida ma kwamishinan Aruwan cewa a yanzu haka yana samu takardar barzana ga rayuwar daga masu garkuwa, inda suke barazanar sace shi da iyalansa.

Haka zalika Shehu ya bayyana ma kwamishinan cewa babu tsaro a majalisar dokokin jahar, hakan ne ma yasa abu kadan sai kaga yan barandan siyasa sun yi kutse har cikin majalisar.

A nasa jawabin, kwamishinan ya roki yan majalisa dasu yi masa afuwa domin kuwa akwai bayanan da ba zai so ya bayyanasu a gaban yan jaridu ba saboda tsaro, don haka ya nemi majalisar ta bashi daman ganawa da ita cikin sirri, a nan zai zayyana maat duk kokarin da gwamnati ke yi game da tsaron jahar Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel