Ba za’a taba daina garkuwa da mutane a Najeriya ba – Inji Gwamna Wike

Ba za’a taba daina garkuwa da mutane a Najeriya ba – Inji Gwamna Wike

Gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa satar mutane da garkuwa dasu ba zai kare a Najeriya ba sakamakon ya zama hanyar samun kudi ga wasu tsirarun miyagun mutane.

Jaridar Punch ta ruwaito Wike ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba a fadar gwamnatin jahar dake Fatakwal yayin daya karbi bakuncin kungiyar Rotary International District 1941, inda yace sai dai kawai a yi abinda za’a iya.

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun kona barayin wayar salula 2 kurmus a jahar Delta

“Ba zai taba yiwuwa a daina satar mutane a Najeriya ba, ya riga ya zama wani sabon kasuwanci, hanyar samun kudi. Sai dai kawai kowa da kowa a taru a hada kai da gwamnati don ganin an rage shi, amma ba za’a iya kawar da shi gaba daya ba.

“Kalli abinda ke faruwa a duk fadin kasar, satar mutane ta mamaye kowacce jaha, a kwanakin baya ma an sace Alkalin kotun daukaka kara a garin Bini, kafin shi ma, an dauke Alkalin babbar kotun tarayya, don haka dole ne mu tsaya mu gam un dakatar da lamarin.” Inji shi.

Gwmana Nyesom Wike ya yi kira ga Rotary da ta fara wayar da ka al’umma, musamman matasa game da illolin da haddura dake tattare da garkuwa da mutane da ayyukan kungiyoyin asiri.

Sa’annan gwamnan ya yi kira ga jama’a dasu kasance masu lura da ankara da unguwanninsu, tare da daukan matakn kare kansu, musamman duba da cewa barayin mutanen suna amfani ne da yan uwa da abokai wajen samun bayanan sirri game da mutum.

Daga karshe gwamnan ya yi alkawarin cigaba da kashe kudi a harkar tsaro a jaharsa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel